Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bayan hutawa ta dan gajeren lokaci a bangarorin harda da kira makaranta biyar ne suka kara da juna har aka fitar da wadanda suka lashe gasar daga na daya zuwa na uku.
A Bangaren harda Mujtaba Fardani shi ne ya zo na daya daga Iran, sai kuma na biyu shi ne Haruna Muhammadu Hassan daga Nijar, sai na uku Muhammad Hamidi Hana daga Indonesia.
A bangaren kira’a ma haka nan na farko shi ne Mahdi GholamNejad daga Iran sai kuma na biyu Muhammad Ali Furughia daga Afghanistan, da kuma na uku hmad Jamal Kamal Almansarawi daga Iraki.