IQNA

23:50 - May 01, 2018
Lambar Labari: 3482620
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman bayar da horo kan kur’ani a birnin Brussels na Belgium.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daidai lokacin gudanar da tarukan Nisf Sha’aban ne za a gudanar da taro kan kur’ani a birnin Brussels tare da halartar malamai.

Wannan dais hi ne karo na farko da ake gudanar da irin wannan taro wanda zai kasance tare da bukukuwan tunawa da zagayowar lokacin haihuwar Imam Mahdi (AJ) a birnin na Brussels, wanda zai hada da jawaba da malamai za su gabatar da kuma kasidu.

Haka nan kuma baya ga bayanai akwai baje koli na kayan tarihin musulunci wanda zai hada da hotunan wuraren tarihi da kuma wasu alluna da suke dauke ba bayanai na addini a kan wannan rana ta daren sha biyar ga watan Sha’aban.

3710963

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: