IQNA

23:53 - May 01, 2018
Lambar Labari: 3482621
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa yariman Saudiyya Bin Salman a shirye yake ya kasha ko dala biliyan nawa ne domin yaki a kasar Iran.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani jawabi da ya gabata a yammacin yau, Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, Bin Salman a shirye yake ya kasha ko dala biliyan nawa ne domin zuga Amurka da Isra’ila su shiga yaki da Iran, wanda ko shakka babu az su sha kayi.

Ya ce duk da cewa har yanzu Saudiyya ba ta yi nasara a dukkanin yake-yaken da ta haddasa a kasashen laraba na yankin gabas ta tsakiya ba, amma kuma a shirye take da ci gaba da bayar da biliyoyin daloli domin bude wasu sabbin fagagen yake-yaken.

A kwanakin baya ne dai Trump ya bayyana cewa, Amurka ta kashe dala Trilion 7 a banza a yankin gabas ta tsakiya ba tare da ta cimma wani abu domin kawai ta kare wasu kasashe, saboda haka dole ne kasashe masu a gabas ta tsakiya su biya Amurka kudinta.

3711092

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: