IQNA

Wani Malamin Shi'a A Saudiyyah Ya Jaddada Wajabcin Hadin kan Al'ummar Musulmi

22:42 - May 02, 2018
Lambar Labari: 3482623
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Hassan Saffar a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron maulidin Imam Zaman (AJ) ya jaddada wajabcin hadin kai tsakanin dukkanin musulmi shi'a da Sunnah.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yanar gizo na jaridar Juhaina ya habarta cewa, a jawabin nasa Sheikh Hassan Saffar a Husainiyar Naser da ke yankin Saihat ya ce abin da ya hada musulmi ya fi wanda ya raba su, domin kuwa musulunci ne ya hada su, abin da ya raba su kuma sanain fahimta ne kawai kan wasu mas'aloli na ilimi.

A kan haka ya ce babu wani dalili da zai sanya musulmi su ci gaba da zama haka kara zube kawunansu a warwatse, matukar dai alummar musulmi tana son ta dawo da mutunci da matsayinta, to dole ne sai musulmi sun hada kai wuri guda.

Kuma hakan shi ne yafi ya sauki, domin kuwa Allah daya suke bautawa mawa, annabi Muhammad (SAW) shi ne kowa ya yarda da shi a matsayin manzon Allah na karshe, ka'aba guda daya ake ziyarta a lokacin hajji, kur'ani daya ne kowane musulmi ya yi imani da shi, sauran batutuwa kuwa kowa ya rike abin da ya fahimta, amma wadannan su ne asali kuma babu canji a cikinsu.

3711131

 

 

 

 

captcha