IQNA

21:48 - May 17, 2018
Lambar Labari: 3482667
Bangaren kasa da kasa, an girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar karatu da hardar kur’ani a kasar hadaddiyar daular larabawa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar albayan cewa, a jiya an gudanar da taron girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar karatu da hardar kur’ani karo na 9 a kasar hadaddiyar daular larabawa wato UAE.

Muhammad Matar Ka’abi shugaban hukumar kula da harkokin gasar kur’ani na kasar hadaddiyar daula larabawa ya bayyana cewa, a yayin taron na jiya iyalan wadanda suka samu kyutuka da kuma wasu daga cikin jami’ai sun halarci wurin taron.

Mutane 580 ne suka shiga cikin wannan gasa, yayin mutane 295 daga cikinsu ne suka kai zuwa ga zagaye na karshe.

3715269

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: