IQNA

23:59 - May 19, 2018
Lambar Labari: 3482675
Bangaren kasa da kasa, Yusuf Usaimin babban sakataren OIC ya ce, Kasashen Musulmi sun bukaci kafa wata rundinar kasa da kasa don kare yankunan Palasdinawa, bayan zubar da jinin Palasdinawa a zirin Gaza.

Kasashen Musulmi Sun Bukaci Kariya Ga PalastinuKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Wakilan kasashe hamsin da bakawai na kungiyar ta (OIC), da suka yi taron gaggawa jiya Juma'a a birnin Satambul na kasar Turkiyya, sun bukaci kariyar kasa da kasa ga al'ummar Palasdinu, ciki har da bukatar aike wa da runduna kasa da kasa, don kare Palasdinu a cewar sanarwar karshen taron.

Ko baya ga haka sanarwar karshen taron ta yi tir da allawadai da kisan da sojojin sahayoniya 'yan mamaya suka yi wa Palasdinawa musamman a zirin gaza inda sama da Palasdinawa sattin  suka yi shahada a ranar Litini data gabata.

Haka zalika kuma sanarwar bayan taron, ta zargi Amurka da goyan bayan laifukan Isra'ila, da kuma ba ta kariya a kwamitin tsaro na MDD, tare kuma da bayyana maida ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus da sokana da nuna kiyaya ga kasashen Musulmi.

Kasashen musulmin sun kuma yi kira ga MDD, data kafa wani kwamitin bincike na kasa da kasa domin binciken zubar da jini al'ummar ta Palasdinu a zirin Gaza.

 

3715490

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، OIC ، IQNA ، Turkiya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: