IQNA

23:44 - May 24, 2018
Lambar Labari: 3482689
Bangaren siyasa, A lokacin da yake ganawa da manyan jami’an gwamnati da sauran bangarori na al’umma a jiya, jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa; tun bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran, Amurka take ta kulla wa Iran makida iri-iri da nufin rusa tsarin musulunci a kasar, amma har yanzu Amurka ba ta ci nasara ba.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jagora ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yin tsokaci kan matakin da Amurka ta dauka na ficewa daga yarjejeniyar nukiliya, tare da sanar da kakaba wasu sabbin takunkumai a kan kasar Iran.

Ya ci gaba da cewa batun kiyayya mai tsanani da Amurka take nuna wa Iran ba batun bas hi da wata alaka da batun shirin makamashin nukiliya, magana c eta adawar Amurka da musulunci, kuma duk wanda ya ce zai riko da musulunci kamar yadda yake, tare da kin mika wuya ga manufofin siyasar makiya musulunci, abin da zai fuskanta kenan daga Amurka.

Ya ce wannan ba gwamnatin Trump ce kawai haka ba, hatta gwamnatin Obama da sauran gwamnatocin Amurka da suka gabata a kan haka aka gina su.

Dangane da alkawalin da kasashen turai uku da suka rage cikin yarjejeniyar suka dauka na ci gaba da mutunta ta, jagora ya ce dole ne jami’an gwamnatin Iran su samu tabbaci a rubuce, idan kuma bah aka ba, to babu wani amfanin wannan yarjejeniyar domin daga karshe su ma za su bi sahun Amurka ne.

Ya kara da cewa Iran tana da masaniya kan cewa kasashen turai ba su da alkawali, domin kuwa abubuwa da dama sun faru wadanda suka tabbatar mata da hakan, a kan haka Iran ba za ta sake fadawa cikin wani tarkon ba, dole ne komai a yi shi bisa yarjejeniya a rubuce.

A karshen jawabin nasa jagora ya bayyana cewa, Iran ci gaba take samu a kowane lokaci kuma abin da zai faru kenan a nan gaba da yardarm Allah.

3717002

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: