IQNA

23:55 - May 25, 2018
Lambar Labari: 3482692
Bangaren kasa da kasa, sojojin gwamnatin yahudawan Isra’ila a cikin shirin yaki sun killace masallacin quds a yau, tare da daukar kwararan matakai kan masu gudanar da sallar Juma’a.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sojojin yahudawan sun kafa shingaye a kan dukkanin manyan tituna masu isa masallacin Quds mai alfarma, kamar yadda kuma wasu daruruwa daga cikinsu suka killace masallacin, tare da bincika musulmi masu shiga masallacin domin yin sallar Juma’a.

Rahoton ya ce sojojin yahudawan sun hana dubban matasa gudanar da sallar Juma’a a yau a masallacin Quds, inda sukan bar mutanen da shekarunsu suka haura arba’in ne kawai su yi salla a masallacin.
Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan bude ofishin jakadancin Amurka a birnin mai alfarma, lamarin da kasashen duniya ke ci gaba da yin Allawadai da shi.

3717432

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: