IQNA

23:44 - May 27, 2018
Lambar Labari: 3482698
Bangaren kasa da kasa, Timothi Waniyuni wani dan majalisar dokokin kasar Kenya ne kuma kirista, wanda ya halarci taron bude wani babban masallaci na musu tare da nuna kaunarsa ga musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da bikin bude babban masallacin Linda Park a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Wannan masallaci dai yana daga cikin masallatai mafi girma  akasar ta Kenya, wanda zai iya daukar dubban mutane a lokaci guda, baya ga haka kuma an gina wasu wurare na musamman da suke a karkashin masallacin.

Daga cikin abubuwan da masallacin kunsa, bayan wuraren alwalla da kuma makewayi da wuraren wanka na musamman ga masu zama da kuma ibadar itikafi, an gina dakin karatu da kuma makaranta, gami da gidan limamin masallacin.

Najib Bilal shi ne ministan yawon bude ido na kasar Kenya wanda ya kasance a wurin, ya bayyana cewa masallaci wuri na haduwar a’aumma domin ibada da kuma amfanar da juna ta fuskoki da dama, musamman a bangaren zamantakewa, da kuma ilmantarwa, da wayar da kai.

Shi ma a nasa bangaren dan majlaisar dokokin kasar kirista da ya halarci wurin, ya bayyana jin dadinsa matuka, ya kuma bayyana cewa masallaci wuri ne da ya kamata ya zama tamkar wata gada ce da take hada kan mabiya addinai da samar da fahimtar juna musamman tsakanin musulmi da kirista.

3717978

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، halarci ، bayyana ، kirista ، Kenya ، Narobi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: