IQNA

23:54 - May 31, 2018
Lambar Labari: 3482712
Bangaren kasa da kasa, Shugaba Bashar al-Assad, na Siriya, ya yi barazanar yin amfani da karfi kan mayakan Kurdawa dana Larabawa dake samun goyan bayan Amurka.

 

Kamfanin dillancin laraban iqna ya habarta cewa, Assad wanda ke bayyana hakan a wata hira da tashr talabijin ta Rasha ya ce zamu iya yin amfani da karfi don kwato yankunan dake karkashin mayakan a yankin arewa maso gabashin kasar.

Shugaba Assad ya kuma ce a shirye yake ya tattauna da mayakan na FDS, amma idan hakan ya cutura, to zamu tsarkake yankunan da karfi.

A hannu daya kuma shugaban Siriyar ya ce, saura kiris a fafata tsakanin tsakanin dakarun Amurka dana Rasha a kasarsa, saidai an sa'ar kauce wa hakan.

3719327

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، assad ، syria ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: