Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin trtarabictv.tv cewa, a jiya cibiyar Zakat ta musulmin birnin Chicago ta shirya taron buda baki tare da gayyatar daruruwan musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa, a yayin buda bakin bayan karatun kur’ani mai tsarki, an gabatar da jawabai dangane da muhimmancin azumi da kuma matsayinsa a cikin addinin musulunci.
Khalil Damir shi ne shugaban kwamitin na Zakat, wanda kuma ya gabatar da bayani kan matsayin zakka a cikin addinin muslunci.
Baya ga haka kuma an kara jadda wajabcin gudanar da ayyuka na alhairi ga dukkain mutane, musulmi da wand aba usulmi, domin hakan shi ne koyarwar musulunci.