Kamfanin dillancin labaran iqna, ma'aikatar lafiya a yankin Zirin Gaza ta fitar da sanarwar cewa: Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wutan bindiga kan al'ummar Palasdinu da suke fito zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a jiya Juma'a a yankin Zirin Gaza, inda suka janyo shahadar Palasdinawa akalla 4 tare da jikkata wasu fiye da 500 na daban.
Tun bayan kammala sallar Juma'a a Masallacin birnin Qudus a jiya Juma'a al'ummar Palasdinu suka fara gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a yankuna daban daban na Palasdinu.
Kamar yadda a jiya Juma'a ce dai aka gudanar da Ranar Qudus ta Duniya a sassa daban daban na duniya, inda ake gudanar da zanga-zangar lumana da taron gangami domin jaddada goyon baya ga al'ummar Palasdinu da ake zalunta da Masallacin Aqsa da ke fuskantar babbar barazana daga Yahudawan Sahayoniyya 'yan mamaya.