Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sheikh Jabir Taei shugaban bangaren kula da harkokin addini na kasa da kasa a ma’aikatar kula da harkokin addini a Masar ya bayyana cewa, ma’aikatar ta aike da masu tablig 3617 zuwa kasashen duniya a cikin wannan wata na Ramadan.
Ya ce akwai limamai 65 da ma’aikatar za ta dauki nauyin biyansu, akwai wasu kuma guda 77 wadanda kasashen da aka tura su ne za su dauki nauyinsu.
Baya ga haka kuma akwai wasu makaranta kur’ani 93, bayan nan kuma akwai wasu wadanda malamai ne masu wa’azi da fadakarwa, wadanda suke yin wa’azi a masallatai, wanda jimillar adadin wadanda aka tura a bana ya kai 3617.