Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne gwamnan lardin Sharqiyya a Masar ya karrama Umar Muhammad Ibrahim wani yaro mafi karancin shekaru da ya hardace kur'ani kuma makaranci a lokaci guda.
Wannan karamin yaro yana dauke da abubuwa na ban mamaki, baya ga kasancewarsa shekarunsa a halin yanzu ba su wuce 3 ba a duniya, yana Magana da harshen turancin ingilishi da faransanci gami da jamusanci kamar yadda yake yin larabci.
An bayar da lambar girmama ta musamman a gare shi tare da halartar wasu daga cikin malamai da kuma jami'an gwamnati gami jama'ar gari.