IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Harkokin Musulunci A Masar

23:54 - July 05, 2018
Lambar Labari: 3482809
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da taron kasa da kasa kan harkokin musulunci a kasar Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa, ana shirin fara gudanar da taron kasa da kasa kan harkokin musulunci a kasar tare da halartar masana daga sassa na duniya.

Bayanin ya ce wannan taro zai mayar da hankali ne kan muhimman lamurra da suka shafi musulmi a duniya baki daya, musamman ma wadanda suke ci musu tuwo a kwarya da kuma hanyoyin da za  awarware su.

Haka nan kuma za aduba batun yadda za a magance matsalar nan ta yaudarar matasa musulmi da ake yi tare da sanya su cikin harkokin ta'addanci da sunan addini ko jihadi bisa jahilci.

3727870

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha