IQNA

23:55 - August 02, 2018
Lambar Labari: 3482854
Bangaren kasa da kasa, babban baje kolin kur’ani mai tsarki da ake gudanawa a Madina ya samu karbuwa daga dubban alhazai na shekarar bana.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban baje kolin kur’ani mai tsarki da ake gudanawa yanzu haka a birnin Madina yana samu karbuwa daga dubban alhazai na shekarar bana da suke ziyara a birnin Madina mai alfarma.

Bayanin ya ce a wurin wannan baje koli ana nuna nauoin kur’anai da aka buga da inji da kuma wadanda aa rubuta da hannu.

Tarihin ur’anan yana komawa zuwa ga lokuta daban-daban, wasu daruruwan shekaru, wasu kuma gomomin shekaru, daga ciki kuma akwai kwafin kur’anai da suke komawa tun shekaru fiye da dubu da suka gabata.

An fara gudanar da wannan baje kolin ne a shekarar da ta gabata, duk kuwa da cewa hakan ya fuskanci matsaloli da dama sakamakon yadda wasu malaman wahabiyawa suke haramta yin hakan, amma dai an ci gaba da gudanar da shi sakamakon babu wani umarni da ya zo daga mahukunta kan a dakatar da shi.

3735120

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: