IQNA

23:50 - August 05, 2018
Lambar Labari: 3482866
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Muhammad Bin Rashid Al Maktum sarkin Dubai a wani lamari mai ban mamaki da ba a taba ganin irinsa ba, ya caccaki mahukuntan kasashen larabawa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin kamfanin dillancin labara Sputnik na Rasha ya bada rahoton cewa, Sheikh Muhammad Bin Rashid Al Maktum sarkin Dubai, kuma mataimakin shugaban kasa hadaddiyar daular larabawa, a wani lamari da ba a taba ganin irinsa ba, ya soki mahukuntan kasashen larabawa tare da bayyana su a matsayin masu bata lokaci kawai.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na twitter, inda ya ce babban abin takaici ne yadda larabawa suka zama bas u iya tabuka ma kansu komai, sai dai su jira  ayi musu, alhali suna da dukkanin abin da suke bukata domin aiwatar da komai a kasashensu.

Sarkin na Dubai ya yi ishara da yadda suka dogara da kasashen yammacin turai a cikin dukkanin lamurransu, inda ya ce wannan mummunar siyasa ce shugabannin kasashen larabawa suka daukar wa kansu, wadda ba za ta fitar da su ba a nan gaba.

3736106

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: