IQNA

23:57 - August 06, 2018
Lambar Labari: 3482869
Bangaren kasa da kasa, Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan lardunan Sa'adah da Hudaidah da suke kasar Yamen.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, talabijin na  masirah ya watsa rahoton cewa, Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan gidajen jama'a a yankin Al-Hajlah da ke lardin Sa'adah a shiyar arewacin kasar Yamen. Kamar yadda suka kai jerin hare-haren kan yankin Al-Zubaid da ke lardin Hudaidah da ke yammacin kasar.

A kwanakin baya ma jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu munanan hare-haren wuce gona da iri kan asibitin Al-Saurah da kasuwar sayar da kifaye a garin Hudaidah, inda suka kashe mutane fiye da sattin tare da jikkata wasu kimanindai na daban.  

3736294

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، saudiyya ، mutane ، hudaidah ، yemen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: