IQNA

Tunawa Ranar Shahadar Imam Jawad (AS) a Pakistan

23:48 - August 12, 2018
Lambar Labari: 3482885
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron makokin tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Jawad (AS) a garin Kuita na kasar Pakistan.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mabiya mazhabar ahlul bait (AS) a Pakistan cewa, a jiya an gudanar da taron makokin tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Jawad (AS).

Taron ya samu halartar dimbin mabiya mazhabar shi'ar Ahlul bait (AS) da kuma wasu daga cikin mabiya mazhabobi sunni da sufaye.

Imam Jawad (AS) shi en limamin shiriya na iyalan gidan manzon Allah (SAW) na tara, kuma an haife shi a shekara ta 195 bayan hijira, ya kuma yi shahada a shekara ta 220, bayan da khalifan Abbasiyawa na lokacin Mu'utasim ya bayar da umani a saka masa guba a cikin abinci.

3737823

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :