IQNA

23:47 - August 16, 2018
Lambar Labari: 3482896
Bangaren kasa da kasa, za a raba kwafin kur'ani mai tsarki guda miliyan daya ga masu gudanar ayyukan hajjin bana.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a shekarar bana za a raba kwafin kur'ani mai tsarki guda miliyan daya ga masu gudanar ayyukan hajji.

Aikin raba kwafin kur'anin zai shafi haramin Ka'abah mai alfarma da ke makka, da kuma masallacin ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa masu tsarki da ke birnin madina.

Ali Bin hamed Alnafe shi ne shugaban hukumar kula da ayyukan kur'ani a kasar saudiyyah, ya bayyana cewa za su gudanar da wanann aikin ne da nufin yalwata adadin kur'anai a hannun mahajja a wannan shekara.

Haka nan ya kara da cewa, daga cikin kur'anan akwai wadanda an tarjama su a cikin harsuna daban-daban, domin maniyya su iya samun damar karantawa da kuma fahimtar abin da ke ciki.

3739007

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، makka ، madina ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: