IQNA

23:41 - August 25, 2018
Lambar Labari: 3482924
Bangaren kasa da kasa, masallacin mabiya mazhabar shi’a a kasar Kenya zai dauki nauyin taron idin Ghadir.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na ciyar yada al’adun musulunci ya bayar da rahoton cewa, masallacin mabiya mazhabar shi’a a kasar Kenya zai dauki nauyin taron idin Ghadir khom da za a gudanar a mako mai zuwa.

Wannan taro dai zai samu halartar malamai da kuma masana daga bangarori daban-daban, daga ciki kuwa akwai wadanda za su gabatar da jawabi da kuma kasidu kan matsayin wannan rana, da kuma darussan da ke cikinta.

Bayan nan kuma za a gabatar da sallolin azuhura da la’asar a wurin kafin ci gaba da taron.

 

3741075

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: