IQNA

23:43 - August 25, 2018
Lambar Labari: 3482925
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar 'yan jarida ta duniya ta bukaci masarautar Bahrain da ta gaggauta saki shugaban cibiyar kare hakkin bil adama na kasar Nabil Rajab da take tsare da shi da kuma wasu 'yan jarida 16 da suma a ke tsare da su.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kungiyar 'yan jarida ta duniya ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da hukuncin daurin shekaru biyar da masarautar Bahrain ta yanke a kan Nabil Rajab, saboda rubuce-rubucensa da yake yi na fadar gaskiya kan abin da yake faruwa a Bahrain.

Bayanin ya ce kungiyar 'yan jarida ta duniya tana kiran masarautar Bahrain da ta saki Nabil Rajab tare da 'yan jaridar 16 da take tsare da su saboda dalilai na siyasa.

Masarautar mulkin kama karya ta kasar bahrain ta kama shugaban cibiyar kare hakkin bil adama ta kasar Dr Nabil Rabab ne tun bayan wani rubutu da ya yi, inda ya suke irin gudunmawar da gwamnatin Bahrain take bayarwa wajen kisan gillar da Saudiyya take yi wa mata da kananan yara a Yemen, kamar yadda kuma bayyana irin mayuwacin da fursunonin siyasa suke ciki a kasar ta Bahrain.

 

3740951

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: