IQNA

23:25 - September 02, 2018
Lambar Labari: 3482947
Bangaren kasa da kasa, jam'iyyar adawa ta Ikhwanul Muslimin a kasar Mauritania ta nuna shakku kan sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin da kuma na kananan hukumomi da za a fitar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Albaya ta nakalto Muhammad Mahmud Wali Sidi shugaban jam'iyyar Ikhwanul musulmin a kasar Mauritaniya yana nuna shkkun da suke da shi dangane da sakamakon zaben da za a sanar.

Wali Sidi ya ce akwai dalilai da dama da suke tabbatar da cewa an aikata wasu lamurra da suka sabawa ka'ida, da nufin bayar da rinjaye ga jam'iyya mai mulki da kuma sauran jam'iyyun da suke kawance da ita.

Ya bayar da misalin cewa, akwai wasu rumfunan zabe da aka ga wasu daga cikin masu mara baya ga gwamnati suna kada kuri'a ba tare da katin zabe ba, inda ya ce wannan alama ce karara ta neman yin aringizon kuri'u domin jam'iyya mai mulki ta samu nasara.

Haka nan kuma Wali Sidi ya kakkausar suka dangane da kalaman da shugaban kasar ta Mauritania Muhammad Wuld Abdulaziz ya yi a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya ce akwai hadari idan aka bari masu tsatsauran ra'ayin addini suka suka cika majalisar dokokin kasar.

3743296

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: