IQNA

23:59 - September 05, 2018
Lambar Labari: 3482957
Dauki ba dadi tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya a cikin mako guda kacal ya lashe rayukan mutane fiye da sattin tare da jikkata wasu dari da hamsin na daban.

 

Kakakin cibiyar kula da ayyukan jin kai a fannin kiwon lafiya a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya Isamah Ali ya bayyana cewa,dauki ba dadi tsakanin kungiyoyin da suke dauke da makamai a birnin Tripoli fadar mulkin Libiya da kuma gefen kudancin birnin kasar a cikin mako guda kacal ya lashe rayukan mutane tare da jikkata wasu 159 na daban, baya ga tilastawa iyalai  da dama tserewa daga muhallinsu.

A gefe guda kuma majiyoyin watsa labaran Libiya sun sanar da cewa, a cikin 'yan watannin nan an sace matan aure sha daya da budurwaye ashirin da daya a yankuna daban daban na kasar ta Libiya.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Libiya ta fitar da rahoton cewa, a Shekara ta dubu biyu da sha bakawai  da ta gabata an samu rahotonnin sace mutane da yawansu ya kai dubu da dari hudu a sassa daban daban na kasar.  

 

3744309

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Libya ، Tripoli ، rikici
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: