IQNA

22:35 - September 14, 2018
Lambar Labari: 3482984
A cikin wani rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar kan yaduwar cutar kwalara a wasu yankunan jamhuriyar Nijar a cikin 'yan watannin baya-bayan nan, an bayyana cewa mutane 55 ne suka rasa rayukansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban ofishin kula da ayyukan jin kai na majalisar majalisar dinkin duniya ya sanar da cewa, bisa alkalumman da suka samu ya zuwa yanzu tun bayan bullar cutar kwalara a wasu yankunan na jamhuriyar Nijar a cikin watan Yunin da ya gabata, akalla mutane 55 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da cutar.

Rahoton ya ce an fara samun bullar cutar kwalara ne a wasu yankuna da ke cikin jahar Maradi, kafin daga bisani ta bazu zuwa wasu yankunan da suka hada da Doso, Tawa da kuma Zinder.

Mutane 2752 aka tabbatar ad cewa sun kamu da wannan cuta a jamhuriyar Nijar tun daga watan Yunin da ya gabata ya zuwa yanzu, yain da mahukunta akasar tare da bangarori na kasa da kasa suke yin iyakacin kokarinsu domin kawo karshen matsalar.

A cikin shekara ta 2017 da ta gabata, majalisar dinkin duniya ta bayar da rahoton cewa, an yi fama da cutar kwalara a kasashe 17 na Afrika, inda mutane kimanin dubu 150 suka kamu da cutar, yayin da kimanin mutane 3000 suka rasa rayukansu.

3746723

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: