IQNA

0:00 - September 18, 2018
Lambar Labari: 3482993
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Masar sun dauki matakin cewa a ranakun ashura za su rufe masallacin Imam Hussain (AS) da ke birnin Alkahira.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wasu majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa, jami’an tsaron kasar Masar za su rika rufe masallacin Imam Hussain (AS) da ke birnin Alkahira a cikin kwanai na makokin Ashura.

Majiyar ta ce ta nakalto daga jami’an ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar cewa; an dauki wannan matakin ne domin bayar da kariya ga wannan wuri mai albarka.

Wannan mataki na zuwa ne bisa hujjar cewa a kowace shkara mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) da aka fi sani da ‘yan shi’ar Ahlul bait, suna gudanar da tarukan makokin juyayin shahadar Imam Hussain (AS) a wannan wuri, amma ana tsoron kada ‘yan salafiyya masu bin akidar wahabiyanci da suke tsananin kiyayay da su, za su iya afka musu a lokacin tarukan, wanda hakan zai jawo bata kashi a tsakaninsu a wannan wuri.

Tun mabiya mazhabar shi’a shi suke gudanar da tarukan a masallacin Imam Hussain (AS) da ke birnin Akahira tsawon daruruwan shekaru ba su taba tayar da hankalin wani ba, bil hasali ma jama’ar yankin suna shiga taron domin a yi juyayin da su, sai a wannan karo ne gwamnatin Alsisi ta dauki wannan mataki.

A gefen masallacin akwai wani wuri da aka ce an bizne kan Imam Hussain, kamar yadda akwa wasu kasashen ma da ake da wasu wuraren da ake yin wanan da’awa, amma dai abin da ya tabbata a tarihi shi ne kansa mai daraja yana birnin Damascus na kasar Sham wato siriya a yanzu.

3747922

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: