IQNA

23:57 - September 22, 2018
Lambar Labari: 3483004
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin wajen kasar Iran Ya bayyana cewa masu daukar nauyin ta’addanci a yankin gabas ta tsakiya ne suke da hannu a harin Ahwaz.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da ya rubuta a shafinsa na twitter, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif Ya bayyana cewa, wadanda suke daukar nauyin ta’addanci a yankin gabas ta tsakiya ne suke da hannu a harin Ahwaz a yau.

Ya ci gaba da cewa wadanda suke daukar nauyin ‘yan ta’addan takfiriyya daga cikin kasashen yankin, su ne suka dauki nauyin horar da su, da kuma ba su makudan kudaden domin wannan aiki.

Haka nan kuma wannan ‘yan ta’adda da masu daukar nauyinsu dukkaninsu yaran Amurka ne.

3748890

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: