IQNA

23:49 - September 29, 2018
Lambar Labari: 3483020
Girgizan kasa mai karfin ma'aunin Richter 7.5 ta aukawa garin Sulawesi na bakin teku a kasar Indonasia a jiya Jumma'a wanda ya haddasa igiyar ruwa mai karfi wacce kuma ta fadawa garin ta kuma kashe kimani mutane dari hudu ya zuwa yanzu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, saurin igiyar ruwan wacce ake kira tsunami ta kai kilomita dari takwas a ko wace sa'a sannan ta na da tsawon mita shida. 

Ambaliyar ruwan da tsunamin ta jawo ya rusa gidaje, tituna da gadoji a yankin, banda haka sun jawo katsewar wutan lantarki da kuma wayar tarko a yankin.

Jami'an bada agajin gaggawa sun bayyana cewa mutane dari uku da tamanin ne aka tabbatar da mutuwarsu sannan wasu dari biyar da arbain suka ji rauni a yayinda wasu 29 suka bace.

Shugaban kasar ta Indonasia ya ziyarci wurin don ganewa idanunsa irin halin da mutanen yankin suka shiga ciki. An rufe tashar jiragen sama na yankin a jiya jumma'a sanadiyyar lalacewar da kayakin aiki a wajen suka yi sanadiyar girgizan kasar da Tsunami.

Amma ana saran za'a bude shi a yau Asabar don samun damar kai kayakin agji na gaggawa wadanda suka hada da abinci da ruwan sha.

3751139

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Indonesia ، Asabar ، gaggawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: