IQNA

Kisan Khasoggi Ya Jefa Saudiyya Cikin Gagarumar Matsala

23:19 - October 17, 2018
Lambar Labari: 3483050
Bangaren kasa da kasa, Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya isa birnin Ankara na kasar Turkiya, domin ganawa da jami'an gwamnatin kasar ta Turkiya kan zargin kashe Jamal Khashoggi.

 

Kamfanin dillancin baran iqna, bayan kammala ziyarasa a Saudiyya tare da ganawa da sarkin kasar da kuma dansa Muhammad bin Salman, a yau kuma Mike Pompeo ya isa kasar Turkiya.

Bayan isarsa Turkiya, a yau Pompeo ya gana da shugaban Turkiya Rajab Tayyib Erdogan, kuma zai gana da ministan harkokin wajen kasar Jawish Auglo.

Babban abin da ziyarar take dauke da shi dai shi ne kokarin yin aiki tare tsakanin Amurka, Turkiya da kuma Saudiyya, domin samo wata hanya wadda za ta kubutar da gwamnatin Saudiyya daga zargin kisan Jamal Khashoggi. 

Wasu majiyoyin gwamnatin Amurka sun tabbatar wa jaridar Washington Post cewa, daga cikin abin da bangarorin uku suke kokarin yi a yanzu, har da dora alhakin kisan Khashoggi a kan wadanda aka tura suka aikata kisan, tare da bayyana wa duniya cewa babu hannun gwamnatin Saudiyya  a ciki, kuma za a hukunta su kan hakan, ta yadda maganar za ta wuce ba tare da tuhumar Sarkin Saudiyya ko dansa Muhammad Bin Salman a kan batun ba, sakamakon yadda kasar take fuskantar matsin lamba daga ko'in a cikin a halin yanzu a kan wanan batu.

3756709

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :