IQNA

23:53 - October 18, 2018
Lambar Labari: 3483054
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar magajin garin brnin Qahriman Mar’ash a Turkiya ta raba wafin kur’ani dubu 20 a Sudan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ma’aikatar magajin garin brnin Qahriman Mar’ash na kasar Turkiya ta raba wafin kur’ani dubu 20 a Sudan mai sunan bugun madaris Rahmat.

Bayanin ya ci gaba da cewa an gudana da bikin karba wadannan kwafin kur’anai a birnin Khartum fadar mulkin kasar ta Sudan, inda jami’ai daga bangarorin biyu suka taru.

An raba wasu daga cikin wadannan kur’anai ga wasu daga cikin masallatan kasar, yayin da kuma wasu aka raba su ga dakunan karatu da kuma wasu cibiyoyin addini gami da makarantu.

Wasu daga cikin cibiyoyin adini a kasar Turkiya ne sukan dauki nauyi bugawa da kuma raba kwafin kur’anai da ma wasu littafai na addi a kasashen musulmi.

3756628

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: