IQNA

23:54 - October 21, 2018
Lambar Labari: 3483062
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Azhar da ke kasar Masar za ta dauki nauyin bakuncin taro mai taken muslunci da kasashen yammaci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daga gobe ne za a fara gudanar da wani zaman taro wanda cibiyar Azhar da ke kasar Masar za ta dauki nauyin bakuncinsa, taron wanda aka yi ma taken muslunci da kasashen yammacin duniya.

Wannan taro dai zai samu halartar masana daga kasashen turai da kuam wasu daga cikin nahiyar Asia, inda za a tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi musulmi musamman mazauna kasashen da ba su da rinjaye.

Babbar manufar taron ita ce samo hanyoyin kara samar da fahimtar juna tsakanin sauran al’ummomi da kuma muuslmi da suke rayuwa  akasashensu, musamman kasashen turai, inda musulmi suke fuskantar matsaloli saboda addininsu.

Baya ga haka kuma za a duba yadda za  akara fadada alaka tsakanin ciboyoyin addini na wadannan kasashe da kuma musulmin da suke zaunea  kasashen, ta yadda za su rika samun damar gudanar da addininsu cikin ‘yanci da kuma kariya daga cibiyoyin addini da suke da tasiri a kan gwamnati da jama’a.

3757528

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، wadannan ، kamfanin dillancin labaran iqna ، musulunci ، gwamnati
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: