IQNA

Bayanan Sirri Na Ci Gaba Da Bayyana kan Kisan Khashoggi

23:57 - October 21, 2018
Lambar Labari: 3483063
Bangaren kasa da kasa, Wani babban jami'i a cikin gwamnatin Saudiyya ya fallasa yadda aka shirya kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi.

 

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a cikin wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labaran reauters wani babban jami'in gwamnatin Saudiyya ya fallasa asirin yadda aka shirya kisan gillar da aka yi wa dan jaridar kasar ta Saudiyya Jamal Kashoggi.

Jami'in ya ce mataimakin shugaban hukumar liken asirin kasar at Saudiyya Ahmad Asiri shi ne ya umarci mutane 15 daga cikin jami'an tsaron kasar da su aiwatar da wannan kisan gilla, bayan da yarima mai jiran gado na kasar Muhammad Bin Salman ya bukaci hakan daga gare shi.

Daga bisani bayan da asirin hakan ya tonu, gwamnatin Saudiyya tare da gwamnatin Amurka suna hankoron ganin an rufe maganar, tare da dora alhakin hakan a jami'an da suka aiwatar da wannan umarni na kisan gillar da aka yi wa Khashoggi, da suka hada har da shi kansa Ahmad Asiri.

3757627

 

 

 

captcha