IQNA

Gyaran Tsohon Masallacin Tarihi Na Kasar Habasha

22:27 - October 24, 2018
Lambar Labari: 3483071
Bangaren kasa da kasa da kasa, an gudanar da gyaran masallacin tarihi na kasar Habasha.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da gyaran masallacin tarihi na Najjashi a kasar Habasha.

Bayanin ya ce wannan masallaci na daya daga cikin masallatai mafi jimawa  a nahiyar Afrika, wanda ake gain tarihinsa na kmawa ne tun lokacin da sahabbai suka yi hijira daga Makka zwa Habasha, bayan da sarkin Habasha na lokacin wato Najjashi ya ba su dama da su yi addininsu a duk inda suke so a cikin kasrsa.

Bisa wasu ruwayoyi, kabrukan wasu daga cikin sahabban da suka yi hijira a lokacin a cikin harabar wannan masallaci ne mai tsohon tarihi.

Sarki Najjashi dai shi ne sarki kirista da ya karbi musulmi a hijira ta farko bayan da kafiran Makka suka tsananta wajen cutar da musulmi, inda anzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa ya umarni mabiyansa da su tafi Habasa, domina  can akwai wani sarki wanda ba a yin zalunci a wurinsa.

3758329

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، habasha ، masallaci ، Najjashi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :