IQNA

Taron Arbaeen Na Imam Hussain (AS) Tare Da Halartar Jagora

23:38 - October 30, 2018
Lambar Labari: 3483082
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron arbaeen na Imam Hussain (AS) tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci a Husainiyyar Imam Khomeni (RA).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau ne aka gudanar da taron arbaeen na Imam Hussain (AS) tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a Husainiyyar Imam Khomeni (RA) da ke birnin Tehran.

A yayin zaman an gabatar da jawabi dangane da irin gudunmawar da Imam Hussain (AS) ya bayar wajen ci gaba da wanzuwar addinin mulsunci na asali bisa koyarwar kakansa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa.

Hojjatol Islam Saadi shi ne ya gabatar da jawabi, inda ya mayar da hankali kan darussan da suke tattare da irin sadaukantarwa da Imam Hussain (AS) a lokacin rayuwarsa mai albarka, da kuma babbar sadaukantarwa da yayi a karshen rayuwarsa.

Haka nan kuma Sa’aadi ya tabo wasu daga cikin jarabawa da Allah madaukakin sarki ya jarabci Imam Hussain (AS) da iyalan gidan manzon Allah da su, kuma suka samu juriya a kan hakan, wanda Allah madaukakin sarki ya karbe sua  matsayin shadidai da suka kare addininsa daga yunkurin azzaluman sarakuna na lokacin da suke da nufin sauya koyarwar wannan addini mai tsarki.

3759988

 

 

captcha