IQNA

23:54 - October 31, 2018
Lambar Labari: 3483087
Bangaren kasa da kasa, a wani sabon farkami da sojojin Najeriya suka kaiwa yan shia mabiya harkar musulunci mutane fiye da arba’in ne suka Kwanta Dama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar euro news ta nakalto kakakin kungiyar harka islamiya ta tarayyar Najeriya yana cewa harin da sojojin suka kaiwa masu tattakin arba'in na Imam Husain a kusa da birnin Abuja yayi sanadiyyar shahadar mutatne da dama.

Kafin haka a ranar Asabar da ta gabata ma sojojin sun kashe mutane akalla 10 a kusa da babban birnin kasar Abu inji  Malam Ibrahim Musa.

Ya ce yana cikin masu zanga zangar sanda sojojin suka kashe mabiya harkar musulunci, ya ce a lokacin tattakin sun bukaci gwamnatin tarayyar kasar ta sake jagoran harkar wanda ya ke tsare tare da matarsa tun ranar sha uku ga watan Disamban shekara ta dubu biyu da sha biyar.

3760067 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: