IQNA

22:56 - November 03, 2018
Lambar Labari: 3483095
Bangaren kasa da kasa, babban malamin cibiyar Azhar Sheikh Ahmad Tayyib ya aike da sakon taya alhini ga jagoran kiristocin kasar Masar, dangane da harin ta'addancin da mayakan kungiyar Daesh suka kai kansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na bawwaba News ya habarta cewa, a cikin sakon da babban malamin cibiyar Azhar ya aike wa jagoran kiristocin kasar Masar, ya bayyana harin ta'addancin da aka kai mabiya addinin kirista a ranar Juma'a da cewa aiki ne na ta'addanci, wanda dukkanin muuslmin kasar Masar suke yin Allawadai da shi da kakkausar murya.

Ya kara da cewa, babban martanin da al'ummar kasar Masar za su mayar a kan wannan aiki na ta'addanci shi ne su kara hada kansu musulmi da kiristoci wuri guda, domin tabbatar da zaman lafiyar kasarsu.

A ranar Juma'a da ta gabata ce dai aka kai wani harin bam a kan wata motar bas da take dauke da kiristoci a lokacin da suke dawowa daga majami'a Alba'a Samuel, da ke yankin Almina na kasar ta Masar, inda 7 daga cikinsu suka rasa rayukansu, wasu kuma suka samu raunuka.

3760889

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: