IQNA

23:53 - November 04, 2018
Lambar Labari: 3483098
Bangaren kasa da kasa, kotun masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan sheikh Ali Salman.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau kotun masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan shugaban jam’iyyar Alwifaq mai adawa a kasar sheikh Ali Salman, da Hassan Sultan dakuma Al Aswad.

Kafin wannan lokacin da kotun kolin kasar ta bayar da bayani kan rashin sahihancin dukkanin zarge-zargen da masarautar mulkin kma karya ta Bahrain take yi a kan wadannan mutane masu neman gyara ta hanyar lumana  akasar.

3761156

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: