IQNA

20:37 - November 09, 2018
Lambar Labari: 3483114
Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron kasar sun bankado wani yunkurin sace wasu kyallye na dakin Ka'aba da ake nufin kai su Morocco.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin shafaq News ya bayar da rahoton cewa, Jami'an tsaron kasar sun bankado wani yunkurin sace wasu kyallye na dakin Ka'aba da ake nufin kai  su Morocco bayan da aka saka su cikin wata kwantaina,a  gabar ruwa da Dumyat.

Bayanin ya ce, bayan binciken da jami'an tsaron an masar suka yi da na'urori na musamman, sun gano cewa an saka wasu kyallaye guda hudu a cikin wannan kwntaina, inda suka bincika domin gano ko na mene ne.

Daga bisani dai an gane cewa wadannan kyalaye na dakin Ka'aba'a ne da suke a kasar Masar, kasantuwar wasu daga cikin kyallaye da ake yi wa Ka'abaha  ado da su ana dinka su ne a kasar Masar.

Jami'an tsaron dai ba su yi wani Karin bayani ba kan makomar mutumin da yake dauke da wannan kaya.

 

3762338

تلاش ناکام برای قاچاق پرده کعبه
 
تلاش ناکام برای قاچاق پرده کعبه
 
تلاش ناکام برای قاچاق پرده کعبه

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: