IQNA

22:43 - November 16, 2018
Lambar Labari: 3483129
Bangaren kasa da kasa, an kori wani bayahuden Isra’ila bayan shigarsa kasar Kuwait da fasfo na kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin jaridar Quds Alarabi ya bayar da rahoton cewa, jami’an tsaron kasar Kuwait sun kori wani bayahuden Isra’ila mai suna Ben Tezyon, wanda ya shiga kasar da fsfo na kasar Amurka a jiya.

Jami’an tsaron kasar ta Kuwait sun tasa keyar wannan bayahude ne wanda ya shigo Kuwait da sunan shi ba’amurke ne, kuma ya zo ne domin halartar babban baje kolin littafai na duniya da ke gudana a kasar ta Kuwait.

Bayan shigowarsa kasar wasu masu fafutuka sun gane shi, kuma nan da nan suka sanar da hukumomin kasar, kuma suka matsala lamba kana la tilas a kore shi, lamarin da yasa mahukuntan kasar ta Kuwait suka dauki wannan mataki.

Ko shekarar da ta gabata ma dai wannan bayahude ya je kasar Saudiyya, inda ya shiga cikin masallacin manzon Allah da ke Madina kuma ya yi ta daukar hotunan kansa a cikin masallacin yana turawa a shafukan yanar gizo.

3764426

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، turawa ، fasfo ، Madina ، Kuwait
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: