IQNA

23:59 - November 26, 2018
Lambar Labari: 3483154
Kungiyar Al-shabab mai da'awar jihadia kasar Somalia, ta kaddamar da wani hari a safiyar yau a kan gidan wani malamin addini a garin Jalkayur.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau Litinin wata mota da aka shakare da bama-bamai ta shi a kusa da gidan wani malamin addini mai suna Abdul Waliy, wanda gidansa yake hade da wata cibiyar addini da yake jagoranta a garin Jalkayur da ke tsakiyar kasar Somalia.

Wani mutum da yake makwabtaka da wurin mai suna Farah Nur ya sheda cewa, bayan tayar da motar da take dauke da bama-bamai, 'yan bindiga sun kutsa kai a cikin cibiyar da kuma gidan malamin, inda ake ta jin harbe-harbe.

Kungiyar Al-shabab ta sanar da cewa ita ce take da alhakin kai wannan hari, amma kungiyar ba ta bayyana dalilin kai harin ba, kuma mutane sha takwas ne aka tabbatar ad sun mutu.

3767132

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، somalia ، alshabb ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: