IQNA

23:02 - November 29, 2018
Lambar Labari: 3483161
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran ba ta neman fara yaki da duk wata kasa, to amma wajibi ne sojojin Iran su kara irin karfin da suke da shi don jan kunnen duk wani mai shirin wuce gona da iri kan kasar ta Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, agoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da kwamandoji da manyan jami'an sojin ruwa na Iran a yau din nan Laraba lokacin da suka kai masa ziyara don girmama ranar kasa ta sojin ruwa ta Iran inda ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai ba ta da nufin fara yaki da wani, to amma wajibi ne ta karfafa dukkanin karfin da take da shi don hakan ya zamanto hannunka mai sanda ga makiya wajen su cire tunanin kawo wa Iran hari da kuma ci gaba da yi mata barazana.

Ayatullah Khamenei ya ce kasar Iran tana da makiya da yawa a saboda haka ya zama wajibi a yi taka tsantsan a dukkanin bangarori da kuma kara irin karfin da ake da shi ciki kuwa har da karfin da sojojin ruwan suke da shi.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya bayyana jin dadinsa da yadda dakarun sojin ruwan na Iran suke samun ci gaba albarkacin kokari da tsayin dakan dakarun musamman matasan cikinsu.

Kafin jawabin jagora din sai da babban hafsan sojin ruwa na Iran din Rear Admiral Hossein Khanzadi ya gabatar da jawabinsa inda yayi karin haske kan irin nasarorin da aka samu ciki kuwa har da kera jiragen ruwan yaki na Sahand da Damavand masu karfin kai farmaki sosai da kwararrun kasar Iran suka kera.

 

3767890

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: