IQNA

23:06 - November 29, 2018
Lambar Labari: 3483163
Bangaren kasa da kasa, an zabi wasu cibiyoyin muuslmi biyu daga cikin cibiyoyin da suka fi kwazo a kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an zabi cibiyoyin IRDF da kuma Islamic Relief Canada a cikin kungiyoyin 100 da suka fi kwazo a kasar baki daya.

Wadannan kungiyoyi dai suna gudanar da ayyukan jin kai ne da kuma taimakon marassa galihu a ckin kasar ta Canada da ma wasu kasashen duniya.

An gudanar da zaben ne tsakanin kungiyoyin jin kai sama da dubu 86 dake kasar Canada wadanda suke gudanar da ayyukan taimakoa  kasar Canada da kuma kasashen duniya.

Ko shakka babu zaben wadannan kungiyoyi guda biyu na musulmi ya kara tabbatar da cewa musulmin kasar Canada suna taka gagarumar rawa wajen tabbatar wa al’ummar kasar cewa addininsu na zaman lafiya ne da taimakon dan adam ba tare da la’akari da addininsa ko akidarsa ba.

 

3767929

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: