IQNA

Babban Taron Baje Koli Kan Birnin Quds A Istanbul

19:45 - December 09, 2018
Lambar Labari: 3483200
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani babban taron baje koli kan birnin Quds a birnin Istanbul na kasar Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jaridar Yeni Shafak ta kasar Turkiya ta bayar da rahoton cewa, tuna  ranar Juma'a da ta gabata ce aka bude wani babban baje koli da ya shafi birnin Quds, a birnin Istanbul na kasar Turkiya.

Rahoton ya ce, wata cibiya ce mai kula da raya al'adu da tari da ke karkashin ma'aikatar magajin garin birnin Istanbul ta dauki nauyin shirya wannan baje koli, wanda kunshi hotuna da suke nuna rayuwa a birnin Quds tun kafin mamayar turawan Birtaniya, da kuma lokacin mulkin mallakarsu, da kuma bayan sun mika birnin ga yahudawan sahyuniya har zuwa yau.

Wannan baje koli na samun halartar dubban mutane da suka hada da 'yan kasar ta Turkiya da kuma 'yan kasashen ketare, wadanda suke zuwa wurin domin ganin wadannan hotuna da kuma samun karin bayani kan birnin na Quds da kuma masallacin aqsa mai alfarma da ke cikin birnin.

3770548

Babban Taron Baje Koli Kan Birnin Quds A Istanbul

Babban Taron Baje Koli Kan Birnin Quds A Istanbul

Babban Taron Baje Koli Kan Birnin Quds A Istanbul

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، istanbul ، turkiya ، qudus
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha