IQNA

Tunisia Za Ta Hana Yin Amfani Da Masallatai Domin Yin Kamfe Na Siyasa

23:58 - December 18, 2018
Lambar Labari: 3483229
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Tunisia tana shirin kafa wata doka wadda za ta hana yin amfani da masallatai domin yin kamfe na siyasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na alkhaleej.ae ya habarta cewa, a yau Ahmad Azum minister mai kula da harkokin addini a kasar Tunisia ya sanar da cewa, suna da shiri fitar da wata doka wadda za ta hana yin amfani da masallatai domin yin kamfe na siyasa a fadin kasar.

Ya ce za a kamamla wannan tsari daga nan zuwa farkon sabuwar shekarar miladiyya, kafin a fara a iki da tsarin a fadin kasar, domin tabbatar da cewa an kauce wa fakewa da addini domin neman kuri’un jama’a.

Wannan mataki dai na zuwa ne domin kaucewa abin da ya faru a zaben shekara ta 2011 a kasar ta Tunisia, inda 'yan salafiyya masu tsatsauran ra'ayi suka yi ta yin amfani da masallatai domin yin kamfe na siyasa, wanda hakan ya mayar da masallatai wajen hatsaniyar sisaya, lamarin da ya ce hakan ya yi hannun riga da koyar addini.

3773410

 

 

captcha