IQNA

OIC Za Ta Kafa Kwamitin Taimaka Ma Falastinawa 'Yan Gudun Hijira

21:13 - December 21, 2018
Lambar Labari: 3483237
Kungiyar kasashen musulmi ta sanar da cewa, tana da shirin kafa wani kwamitin wanda zai dauki nauyin taimaka Falastinawa 'yan gudun hijira.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kungiyar kasashen musulmi OIC ta sanar da cewa, tana da shirin kafa wani kwamitin wanda zai dauki nauyin ayyukan taimaka Falastinawa fiye da miliyan 5  da suke gudun hijira a ciki da wajen Palassine.

Yusuf Usaimin babban sakataren kungiyar ya bayyana cewa, yanzu haka an gudanar da zama tsakanin kwararru na kungiyar, wadanda suka tattauna tare da fitar da hanoyoyin da za a bi domin taimaka ma Falastinawan.

Ya ce wannan zama dai ya zo ne bayan da majalisar dinkin duniya ta gaza wajen gudanar da ayyukan taimaka ma Falastinawa da suke gudun hijira a ciki da wajen Palastine, bayan da Amurka ta yanke taimakon da take bayarwa domin gudanar da wadannan ayyuka.

A ranar 16 ga watan Janairun wannan shekara ne dai Amurka ta sanar da cewa ta yanke taimakon dala miliyan 300 da take bayarwa domin taimaka ma falastinawa 'yan gudun hijira, wanda hukumar UNRWA ke gudanar da ayyukan.

Akwai Falastinawa miliyan 5.9 da Isra'ila ta kora daga cikin yankunansu, wadanda wasu suna zaune sansanonin 'yan gudun hijira  acikin Palastine, wasu kuma suna ksashe makwabta, da suka hada da Lebanon, Syria da kuma Jordan.

3774294

 

captcha