IQNA

Amurka Ba Ta Yanke Shawara kan batun Ficewa Daga Kasar Afghanistan Ba

23:50 - December 30, 2018
Lambar Labari: 3483265
Fadar White House a kasar Amurka ta sanar da cewa, shugaban kasar Donald Turmp bai bayar da umarnin ficewar sojojin Amurka daga kasar Afghanistan ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cikin bayanin da ta fitar kan wannan batu, fadar white House a kasar Amurka ta bayyana cewa, dukkanin rahotannin da aka yada da ke cewa Trump ya bayar da umarni ga sojojin Amurka da ke kaar kasar Afghanistan da su fara shirin ficewa daga kasar  ba gaskiya ba ne.

Shi ma a nasa bangaren babban kwmandan dakarun Amurka da ke Afghanistan kuma babban kwamandan dakarun NATO a kasar janar Gen. Scott Miller, ya ce ba su samu wani umarni makamancin haka daga shugaban kasar Amurka Donald Trump ba.

Bayan umarnin da Donald Trump ya bayar da ficewar sojojin Amurka daga kasar Syria, wasu rahotanni sun ce shugaban na Amurka zai janye sojojin kasarsa daga kasar Afghanistan, lamarin da ya harzuka wasu daga cikin 'yan majalisar dattijan kasar ta Amurka.

3776403

 

 

 

 

 

captcha