IQNA

Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Kame Falastinawa 15 A Yau

22:48 - January 02, 2019
Lambar Labari: 3483275
Jami'an tsaron Isra'ila sun kame Falastinawa 15 a cikin yankunan da ke gabar yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron an Isra'ila sun kutsa kai ne yau da rana tsaka a cikin yankunan Falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, inda suka kame wasu falastinawa su 15, suka yi awon gaba da su.

Wannan mataki na Isra'ila na zuwa ne a daidai lokacin da take kara fuskantar matsin lamba daga duniya, musamman manyan kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa, dangane da cin zalun da take yi wa Falasinawa.

Daga ranar Litinin da ta gabata ya zuwa yau, a cikin sa'oi kasa a arba'in da takwas, jami'an tsaron Isra'ila sun kame Falastinawa 36, wadanda ba a san inda suka nufa da su ba.

Hukumar Falastinawa da ke bin kadun wadanda Isra'ila take tsare da sua gidan kaso ta fitar da wasu alkalumma dangane da adadin Falastinawan da ake tsare da sua gidajen kason yahudawa, inda alkalumman suka nuna cewa adadin ya haura dubu 6, daga ciki kuwa har da 'yan majalisar dokokin palastine 6, da kuma mata 52, da kananan yara 270, gami da 'yan jarida da ma'aikatan kiwon lafiya da masu fafutuka da dama.

3777935

 

captcha