IQNA

Jami’an Tsaron Iraki Sun Samau Nasar Cafke Kwamandojin Daesh 7

23:54 - January 03, 2019
Lambar Labari: 3483280
Bangaren kasa da kasa, rundunar ‘yan sanda a kasar Iraki ta sanar da cafke wasu manyan kwamandojin kungiyar ‘yan ta’addan daesh su 7 a cikin lardin Karkuk.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da shafin yada labarai na wa’i ya bayar, ya bayana cewa a yau  rundunar ‘yan sanda a kasar Iraki ta sanar da cafke wasu manyan kwamandojin kungiyar ‘yan ta’addan daesh su 7 da ake nemansu ruwa a jallo.

Bayanin rundunar ‘yan sandan ya ce an kame ‘yan ta’addan ne bayan samun cikakkun bayanai na sirri kan wuraren da suke boye a yankin Altun da ke arewa maso yammacin birnin Karkuk.

Rundunar hadin gwiwa mai yaki da ta’addancia  Iraki ta kaddamar da samame a wurin, ta kuma samu nasarar cafke su, bayanin ya kara da cewa kame wadannan giggan ‘yan ta’adda babbar nasara ce, zai kuma zai kara taimakawa wajen gano sauran wadanda ake nema a da suke boye a wasu wurare a cikin kasar bayan tarwatsa su a mausil.

3778208

 

 

captcha