IQNA

Shirin Gina Cibiyar Darul Kur’an A Yammacin Afrika

13:26 - January 30, 2019
Lambar Labari: 3483337
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da ke hubbaren Hussani na shirin gina wata cbiyar Darul Kur’a a yammacin Afrika.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a yunkurin da take yin a ganin an fadada ayyukan kur’ani mai tsarki cibiyar da ke hubbaren Hussani na shirin gina wata cbiyar Darul Kur’a a kasar Burkina Faso.

Bayanin ya ce yanzu haka wata bababr tawaga daga karkashin cibiyar hubbaren ta isa birnin Wagadugu na kasar Burkina Faso, inda tae ganawa da malamai na kasar mabiya ahlul bait, tare da halartar Sheikh Hassan Mansuri shugaban shirin.

Haka nan kuma ana shirin fara gudanar da wani aiki makamancin wannan a gabashin nahiyar Afrika, inda za a bude wata cibiyar warisul anbiya a karkashin wannan shirin, wanda zai gudana a kasar Uganda.

Wannan na zuwa ne bayan gudanar da wasu shirye-shirye na gina cibiyoyin kur’ani da hubbaren Hussani ya yi a kasashen Iran, Lebanon da kuma Indonesia, wanda kuma an samu gagarumar nasara wajen aiwatar da shirin kamar yadda ya kamata.

Tawagar ta ziyarci cibiyar muslunci ta kasa da kasa da ke birnin na Wagadudu a kasar Burkina Faso, wato cibiyar Muzdahar.

3785539

 

 

 

captcha