IQNA

23:40 - February 05, 2019
Lambar Labari: 3483347
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da tarukan zaman makoki na zagayowar lokacin shahadar Sayyidah Fatima Zahra (AS) a Husainiyar Imam Khomeni (RA).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne fara gudanar da tarukan zaman makoki na zagayowar lokacin shahadar Sayyidah Fatima Zahra (AS) a Husainiyar Imam Khomeni (RA) da ke birnin Tehran tare da halartar jagora, da kuma shugaban kasa gam da shugaban majalisar dokoki da kuma alkalin alkalai.

A yayin taron Hojjatol Islam Khatami ya gabatar da jawabi dangane da matsayin rayuwarta da kuma irin darussan da rayuwar wannan baiwar Allah take koyar da dan adam, da hakan ya hada da hakuri, da tsoron Allah, tsentseni son Allah da manzonsa da kuma biyayya gare su hakikanin biyayya.

Haka nan kuma ya yi ishara da yadda lokacin a wannan karo ya zo daidai lokacin da ake gudanar da tarukan cikar shekaru arba’in na samun juyin juya halin musulunci a kasar Iran.

3787954

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: